IQNA

An  Tattauna Batun Hadin kan Musulmi A Rediyon Kasar Uganda

14:26 - November 23, 2020
Lambar Labari: 3485391
Tehran (IQNA) an tattauna batun hadin kan al’ummar msuulmia  wani shrin rediyon kasar Uganda.

A cikin wanda ya samu halartar shugaban ofishin yada aladu na kasar Iran a kasar Uganda da kuma Rashid Key Wanuka, shugaban bangaren sadarwa na majalisar musulmin kasar Uganda, an tattauna batun hadin akn al’ummar musulmi.

Shugaban ofishin yada aladu na Iran a kasar ta Uganda Muhammad Reza Qazalsofli ya bayyana cewa, akwai abubuwa da dama wadanda suke zama babban karfen kafa wajen haduwar kan musulmi a duniya.

Ya ce abin da ya fi jawo haka kuma banbancin fahimta ne kan ams’aloli ba kan addini ba, domin abbu wani sabani a kan asalin addini, imani da Allah da kuma manzancin manzon Allah, babu sabani tsakanin musulmi a kan wannan wannan.

Qazalsofli ya ce, inda ake samun sabanin fahimta shi ne kan sunnah, ko da yadda yake fassara sunnah, wato abin da ma’aiki ya yi ko ya yi uamrni a yi ko kuma yadda shi ya aiwatar, wanda kuma dama wannan abu ne da za a iya samun sabani akansa domin kuwa ruwayoyi ne za su iya zuwa ta hanyoyi daban-daban.

Ya ce abin da yake da muhimamnci shi ne haduwa  akan asalin addini ba far’in addini ba, abin da yake far’i ne kowa ya rike fahimtarsa, amma abun da babu banbancin fahimta a kansa wato asalin addini, a hadu a  yi aiki tare a kansa. 

Shi ma a nasa gefen shugaban bangaren sadawa na majalisar musulmi kasar Uganda ya yi ishara da wani abu day a bayyana shia matsayin wata matsala wadda ta babbar musuiba ga musulmi, shi ne bullar sabbin akidu na takfiriyya, masu kafirta al’ummar musulmi da shelanta jihadi a kan musulmi da wadanda ba musulmi.

Ya ce a akidarsu kowa kafiri ne mushriki ne matukar ba a cikinsu yake ba, wanda kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi suna dauke ne da irin wanna akida, shi yasa za su kai hari coci kuma suka kan musulmi a cikin masallaci har ma a lokutan da ake cikin salla.

 

3936854

 

 

 

 

captcha